Cameron ya sasanta fada kan kasafin kudi

Piraminstan Birtaniya,David Cameron
Image caption David Cameron ya sasanta wasu ma'aikatun kasar

Piraministan Birtaniya David Cameron, ya sasanta wani rikici tsakanin ministocinsa biyu dangane da kasafin kudin da a ke kashewa ta fuskar tsaron kasar.

Baital malun kasar dai na son rage kasafin kudin ma'aikatar tsaro ne, abinda ya kawo cece-kuce tsakaninsa da ma'aikatar tsaro.

BBC ta fahimci cewa Mista Cameron ya tilas baiwa sojoji isasshen kudi don gudanar da aikace aikacen su.

David Cameron ya goyi bayan sakataren tsaro Liam Fox, wanda ya yaki baital malun don ganin ba a rage kasafin kudin ma'aikatar da kashi goma cikin dari ba.

Ana ganin sasantawar ce tasa kasafin kudi a fannin tsaro ya kasance fan biliyan 37 a duk shekara.