Batun cocaine a kasar Bolivia

Shuagabn Bolivia,Evo Morales
Image caption Morales ya amince cewa ana noman koko a kasar domin samar da hodar cocaine

Shugaban kasar Bolivia Evo Morales, ya amince a karon farko cewa wasu daga cikin jiga-jigan magoya bayansa na samar da ganyen koko ga masu safarar hodar cocaine.

A baya dai yayi ta musanta zargin da Amurka tayi na cewa wasu magoya bayansa na sayar da amfanin gonarsu ga masu sarrafa hodar iblis.

An dade da sanin cewa wasu daga cikin ganyayyakin kokon da a ke samar wa a Bolivia na bugewa ne a hannun masu fataucin miyagun kwayoyi.

Sai dai yanzu Mista Morales, wanda ke shugabancin babbar kungiyar manoma koko a Bolivia, ya amince cewa wasu mambobin kungiyar na sayar da amfanin gonarsu a kasuwar bayan fage.

Shugaban ya ce, su kansu manoman sun sani cewa wasu daga cikin ganyayyakin kokon na fadawa hannun masu gudanar da haramtaccen kasuwanci, abinda masu sukarsa,musamman Amurka sukai ta fada shekara da shekaru.

Shekaru biyun da suka gabata, Mista Morales ya kori hukumar da ke sa-ido kan fataucin kwayoyi ta Amurka, inda ya zarge ta da sanya siyasa a cikin batun.Ya ce kasar kadai za ta iya takaita yadda a ke noman kokon.