An gano gawawwaki a Ecuador

Daya daga cikin injiniyoyin da su ke yin aikin
Image caption An gano gawawwaki a Ecuador

Injiniyoyin da ke kokarin kaiwa ga wasu mahaka ma'adinai hudu da suka makale a karkashin kasa a Ecuador, sun gano gawawwakin mutane biyu daga cikin mahakan.

Masu ayyukan ceto na huda rami ta cikin duwatsu bayan da kogon da mutanen ke ciki ya rufta dasu, inda kuma kawo yanzu, babu wata alama da ke nuna cewa sauran mahakan biyu suna raye.

Estefania Alarcon ita ce kakakin gwamnatin kasar.

Ta ce: ''Za mu kawo mutum-mutumi hade da na'urar daukar hotuna a wuraren da a ka kwashe kasar don ganin ko za mu gano sauran mahakan''.