FIFA za ta gudanar da binkice

Shugaban FIFA,Sepp Blatter
Image caption FIFA za ta gudanar da binkice kan jami'anta

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya ta ce, tana binkice kan zargin da a ke yiwa biyu daga cikin mambobin babban kwamatinta na amincewa su sayar da kuri'unsu, kan kasar da za ta dauki nauyin gudanar da gasar a shekarar 2018-2022.

Jaridar Sunday Times ta ce, wani mamba dan Najeriya Amos Adamu, da takwaransa na Tahiti Reynals Temarii, sun shaidawa manema labaran da su ka yi sojan-gona cewa za su sayar da kuri'unsu.

Jaridar ta ce, ta dauki hotunan bidiyo cikin sirri na wata hira da a ka yi da mambobin biyu.

'Za su yi amfani da kudin don ayyukansu'

Jaridar ta ce, an tambayi Amos Adamu shin yana gani idan a ka bashi kudi don gudanar da aikin kashin kansa hakan za ta sa ya sauya yadda zai kada kuri'a, sai ya ce, ''lallai hakan zai yi tasiri.Tabbas kuwa''.

Ya shaidawa 'yan jaridar cewa shi za a baiwa kudin, ba gwamnatin kasarsa ba.

Ya kara da cewa, yana neman hanyar da zai samu kudi kimanin fan dari biyar don gina filayen wasa.

Jaridar ta kuma yi zargin cewa shi ma Reynald Temarii, wanda shi ne shugaban wata gamammiyar kungiyar kwallon kafa, ya tattauna batun biyan sa kudi don gina wata makarantar koyar da wasanni.

Sai dai FIFA ta ce, ta sa ido sosai kan yadda a ke kokawar ganin an dauki nauyin gudanar da gasar, kuma za ta tankade-da rairaye duk wani al'amari kan batun.