Ma'aikata na gudanar da zanga- zanga a Faransa

Zanga-Zangar kasar Faransa
Image caption Dubbunan daruruwan ma'aikata a kasar Faransa na gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewarsu ga shirin da gwamnatin kasar take yi na yiwa tsarin fanshon kasar garanbawul

Dubunnan daruruwan mutane ne ke zanga-zanga a manyan titunan da ke fadin kasar Faransa a cigaba da nuna rashin amincewarsu da shirin gwamnatin kasar na yiwa tsarin fansho garambawul.

Ita dai gwamnatin na kokarin dage shekarun ajiye aiki ne daga sittin zuwa sittin da biyu.

A yanzu haka dai matasalar karancin mai ita ce tafi ciwa gwamnatin kasar tuwo a kwarya. An rufe dukkanin matatun man kasar kuma man zai janye kama daga mako mai zuwa idan har masu daukar man suma suka tsunduma cikin masu zanga zangar

Duk da wannan abu da yake faruwa babu wata alama dake nuni da cewar Shugaba Sarkozy zai sakko daga kan matsayinsa, haka dai suma kungiyoyin maikatan kasar.