Miyetti Allah ta fada rikici

Taswirar Najeriya
Image caption Kungiyar miyetti Allah ta fada rikici

Wata baraka ta kunno kai a kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta kasa a Najeriya sakamakon batun zaben shugabannin kungiyar.

Wannan baraka ta fito fili ne yayin da wasu 'yan kungiyar su ka kira wani taron manema labarai a Kaduna, inda su ka gabatar da zababbun shugabannin kungiyar.

Alhaji Sale Bayere shi aka nada a matsayin sabon sakataren kungiyar na kasa, ya shaidawa BBC cewa:''Ranar daya da biyu ga wannan wata shugabannin fulani su ka hadu a Gombe, inda su ka kawo sakamakon zabukan da suka gudanar a shiyoyinsu, kuma babu wanda ya bayyana rashin amincewarsa za zaben''.

Sai dai jim kadan bayan hakan wani bangaren kungiyar ya karyata ikirarin gudanar da zabe a kungiyar, inda ya ce kungiyar ta dade bata da wasu shugabanni a sanadiyyar rikice rikice na shugabanci.

Bangaren ya ce, bai san ranar da aka gudanar da wani zabe ba.

Alhaji Bello Liman Shehu shi ne shugaban Miyetti Allah na jihar Zamfara, kuma ya ce:''Ba mu san an yi zabe ba.Kowa ya biya kudin sayen fom na takara, sai mu ka ji kwatsam jiya wai za a yi taro, sakamakon zaben da aka yi a Gombe.Abinda suka yi kuskure ne''.