Kasashen Afirka hudu zasu yaki 'yan tawayen LRA

Sojojin gamayyar kasashen Afirka
Image caption Kasashen Afirka hudu zasu kafa wata rundunar sojin hadin gwiwa da zata fafata da 'yan tawayen LRA

Gamayyar kasashen Afrika ta baiyana cewa kasashe hudu zasu kafa rundunar sojin hadin gwiwa da za ta fafata da 'yan tawayen Lord's Resistance Army, LRA, wacce ta kwashe shekaru biyu ta na kai hare-haren sari-ka-noke a yankunansu tare da tilastawa mutane dubu dari hudu kauracewa daga gidajensu.

Kasashen Sudan, da jamhuriyar dimokradiyyar Congo, da jamhuriyar Afrika ta tsakiya, da kuma Uganda ne zasu kafa wannan rundunar domin kalubalantar mayakan LRA wacce ta samo tushe shekaru ashirin da suka wuce a Uganda.

An cimma wannan matakin ne a tattaunawar da kasashen suka yi a Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.