Yaki da masu sace sacen mutane a Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Rundunar sojin Najeriya ta kama mutane 100 da take zargin masu aikace aikacen sace mutane ne a jahar Abia dake kudu maso gabacin kasar

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana kame kimanin mutane dari da ake zarginsu da fashi da makami da kuma satar mutane da zummar neman fansa, a Jihar Abia.

Rundunar sojin, karkashin jagorancin Manjo Janar Sarkin Yaki Bello ta bayyana cewa daga ranar daya ga watan Oktobar da muke ciki zuwa yau, ta kama wadannan mutanen, ciki har da wani shugaban coci da take zargin na da hannu a wannan aika-aikar.

Kama mutanen dai ya biyo bayan wani samame da jami'an tsaro suka kai a wurare daban daban a jihar ta Abia, a wani yunkuri na daukar mataki, bayan kaurin suna da jihar ta yi akan yawaitar masu aikata muggan laifuka iri iri.

Ko a kwanakin baya, sai da aka sace wadansu 'yan jaridu da kuma wasu yara 'yan makaranta a jihar da zummar neman kudaden fansa.