Za a tisa keyar James Ibori zuwa Birtania

James Ibori
Image caption James Ibori

Wata kotu a Dubai ta yanke hukuncin cewar a tisa keyar tsohon gwamnan Jihar Delta da ke yankin kudu maso kudu a Najeriya, watau Mr James Ibori zuwa Birtaniya.

A Birtaniya dai ana neman Mr James Ibori ne domin ya fuskanci tuhumar da ake yi masa ta sama da fadi da kudaden jama'a da kuma halatta kudaden haram.

'Yan sandan Hadaddiyar Daular larabawar ne dai suka tsare Mr James Ibori a watan Mayun daya gabata.

Hukumar EFCC a Najeriya wacce ke farautar Mr. James Iborin tace hukuncin bai zo mata da mamaki ba.

Rahotanni sun ce Mr James Ibori ya ce zai daukaka kara akan wannan hukunci.

Tuni wata Kotu a Birtaniya ta samu wasu mutane da ke da alaka da Mr James Ibori da laifi akan halatta kudaden haram.