An kama dan uwan Henry Okah

Henry Okah
Image caption Henry Okah

Ma'aikatan tsaro a Nigeria sun cafke dan uwan tsohon jagoran kungiyar nan mai fafutukar kwato 'yan cin yankin Niger Delta, watau MEND.

An kama Charles Okah ne, watau dan uwa ga Henry Okah a birnin Ikko bisa zargin samu hannu a hare haren bama bamai da aka kai a birnin Abuja ranar daya ga watan Octoba.

Wani bangare na kungiyar MEND, wanda bai amince da shirin ahuwa na gwamnatin Nigeria ba ne ya dauki alhakin kai hare haren.

Hukumar ma'aikatan tsaro ta SSS da ke gudanar da bincike akan harin ta kuma zargi jagoran yakin neman zabe na Janar Ibrahim Babangida watau Chief Raymond Dokpesi da samun hannu a hare haren.

Kalaman da shugaba Goodluck Jonathan yayi, inda ya wanke kungiyar MEND da kai hare haren yana cewar wasu 'yan ta'adda ne suka kai harin na Abuja, ya haddasa kace-nace.

Mutane akalla goma ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunika a harin da aka kai gab da dandalin Eagles Square, inda aka gudanar da bukin cika shekaru 50 da samun 'yan cin kan Nigeria daga turawan mulkin mallaka.