Tsuke bakin aljihu zai shafi jiragen Burtaniya

Sakataren Tsaron Burtaniya, Liam Fox
Image caption Sakataren Tsaron Burtaniya, Liam Fox

Sakataren Tsaro na Burtaniya, Liam Fox, ya bayyana cewa manyan jiragen ruwa masu daukar jiragen saman yaki guda biyu wadanda kasar ke kerawa—duk kuwa da zaftare kudin da gwamnati ke kashewa a kan al'amuran tsaro—za su kasance ba jiragen saman har wani lokaci.

Wannan sanarwar dai ta zo ne a farkon makon da ake sa ran gwamnatin ta Burtaniya za ta fayyace sababbin manufofinta na tsaro, ta kuma bayar da sanarwar wani gagarumin matakin tsuke bakin aljihu.

Burtaniya dai na fuskantar matakan tsuke bakin aljihu mafi girma a shekaru da dama, kuma ya zuwa yanzu harkar tsaro na cikin bangarorin da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu.

Babban Ministan Kudi na kasar, George Osborne, ya bayyana cewa kera sababbin manyan jiragen ruwan yakin na cikin shawarwarin da ya yanke masu matukar nauyi yayin da ya ke nazari a kan matakan tsuke bakin aljihun.

Sai dai, a cewarsa, soke aikin kera jiragen ruwan zai ci kudi fiye da ci gaba da aikin.

Yanzu dai ta bayyana cewa mai yiwuwa jiragen ruwan za su kwashe shekaru ba tare da jiragen saman yaki ba.

Hakan kuma ba zai rasa nasaba da gibin da za a samu ba tsakanin daina amfani da tsofaffin jiragen yakin kasar da kuma lokacin da za a dauka kafin kammala sababbin.

Ranar Juma'a Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta bayyana damuwarta dangane da rage yawan kudin da Burtaniyar ke kashewa a kan harkar tsaro.