An kashe 'yan bindigar da suka kai hari a Chechenya

Jami'an Rasha sun ce an hallaka dukan 'yan bindigar da suka afkawa ginin majalisar dokoki a Grozny, babban birnin jamhuriyar Chechnya da ke kudancin Rashar.

A kalla wasu mutanen ukku kuma sun rasa ransu.

An kai harin ne yayin da 'yan majalisar dokokin ke zuwa wurin aiki.

Da alama dai maharan sun bi jerin gwanon motocin jami'ai ne suke wuce tsauraran matakan tsaron da ake da su a kofofin shiga majalisar dokokin kafin daga bisani su tayar da bama-baman da suka haifar da barna a majalisar.

Mutane da dama ne dai suka samu raunuka sakamakon rudanin da ya biyo bayan fashe-fashen.

Kabbara

'Yan majalisar dokokin da suka nemi mafaka a cikin ginin majalisar, sun ce sun ji maharban suna ta kabbara, a lokacin da suke harbin kan mai uwa da wabi.

Sai dai jami'ai a Chechenyan sun ce an jami'an tsaro sun kashe dukkan 'yan bindigar.

Ministan cikin gidan kasar rasha Rashid Nurgaliyev, ya ce, "'yan bindigar sun yi kokarin kutsa kai cikin majalisar da karfin tsiya. Kamar yadda aka saba, ba su samu nasara ba. Jami'an ma'aikatar cikin gida sun hana su, kuma sakamakon haka an kawar da dukkan 'yan bindigar."

Jami'ai a yankin sun ce an kashe masu gadi uku da farar hula daya a harin.

Wani mai magana da yawun majalisar ya ce bayan shafe kusan mintuna ashirin ana bata kashi, an kai 'yan majalisar dokokin tudun mun tsira.

Harin dai wani abun damuwa ne ga kasar rasha da mutumin da ta dogara da shi a yankin Ramzan Kadyrov, saboba ikirarin da suka yi a baya na cewa sun dakile tayar da kayar baya a yankin.