Xi Jinping ya samu karin girma a China

An yi karin girma ga mataimakin shugaban kasar China, Xi Jinping , zuwa wani babban mukamin soji -- wanda mutane da yawa ke kallo - a matsayin wata kyakkyawar dama ta zama shugaban kasa.

Da ma an dade ana kallon Mr Xi a matsayin wanda zai iya gadar Shugaba Hu Jintao -- wanda ake sa ran zai sauka a shekara ta dubu 2012.

Jam'iyyar kwaminisanci ta kasar ta China, ce ta yi ma sa karin girmar.

Shi ma shugaba Hu Jintao, ya taba rike wannan mukami kafin ya zamo shugaban kasa.