EFCC za ta kame 'yan takara a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Yayin da zabuka ke kara matsowa a Najeriya, Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa, wato EFCC, ta ce ta dukufa domin ganin cewa wadanda ke aikata cin hanci da rashawa ba su tsaya takara a zabukan da ke tafe ba.

A cewar Hukumar, yin hakan ya zama wajibi saboda yadda wadansu shugabanni a kasar ke yin almubazzaranci da dukiyar kasar, yayin da talakawa ke kokawa da rashin abubuwan more rayuwa.

Mataimaki na musamman ga Shugabar Hukumar, Abubakar Uthman, ya shaidawa BBC cewa “duk wani dan takara wanda mu[ka] san shi da datti wallahi bai shiga [takara]; in ya shiga kuma ko a wajen rantsar da shi sai mun je mun kame shi”.

Hukumar ta EFCC dai ta ce tana tuntubar takwararta ta ICPC, da hukumar zabe ta INEC, da bangaren shari'a, da kuma sauran hukumomi na tsaro a kasar domin cimma wannan buri nata, kuma tana gudanar da taruka na fadakar da jama'a a duk fadin kasar domin kada jama'a su zabi mutanen da ke wawure dukiyar jama'a.

Sai dai wadansu 'yan adawa na ganin ana so ne kawai a yi amfani da hukumar ta EFCC domin a muzguna masu, zargin da hukumar ke musantawa.