Sarkozy ya cije game da zanga zangar da ake a Faransa kan tsarin fansho

Shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, yace zai ci gaba da aiwatar da sauye sauye kan tsarin pansho, dukkuwa da zanga zangar da ake tayi a kasar.

Mr Sarkozy ya ce sauye sauyen da suka hada da kara shekarun ritaya daga sittin zuwa sittin da biyu na da amfani sosai.

Direbobin manyan motoci da ma'aikatan kamfanonin mai na ta datse hanyoyi da depo-depo na man petur

Shugaban kungiyar direbobin manyan motoci, Thierry Cordier ya ce tun da Gwamnati ta toshe kunnuwanta, ba ta ji ba ta gani, to kuwa ta ga abinda zai faru a kasar.

Tuni wasu gidajen mai fetur din suka fara karancin. Zanga zangar a wasu wuraren ta rikida ta zama rikici.

Ma'aikatar zirga zirgar jiragen sama ta bada umurnin soke akalla kashi talatin cikin dari na jiragen da zasu tashi gobe, saboda wannan matsala.