FIFA na bincikar zargin cin hanci

Amos Adamu na hukumar FIFA
Image caption Amos Adamu ya dade yana taka rawa a fagen kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA, na bincikar manyan jami'anta biyu bisa zargin yunkurin sayar da kuri'arsu ga daya daga cikin kasashen da ke son daukar nauyin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018.

Shugaban hukumar Sepp Blatter, ya ce badakalar na da "mummunan tasiri" ga martabar hukumar ta FIFA.

Wasu ma'aikatan jaridar Sunday Times ta Burtaniya ne suka yi shigar burtu a matsayin ma'aikatan wani kamfani da ke kokarin ganin Amurka ta samu nasarar daukar nauyin gasar.

Sun yi zargin Amos Adamu daga Najeriya da Reynald Temarii dan kasar Tahiti sun nemi su sayar da kuri'un su.

Adamu, wanda mamba ne a kwamitin gudanarwa na FIFA, an ce ya nemi a bashi dala 800,000 domin ya gina wasu filayen wasa na zamani guda hudu.

Hakan kuwa ya sabawa dokokin hukumar FIFA.

'Za su yi tasiri sosai'

Rahotanni sun kara bayyana cewa za kuma a binciki biyu daga cikin kasashen da ke neman daukar nauyin gasar.

Hotunan bidiyon da jaridar Times ta wallafa sun nuna Mista Adamu yana bukatar a biya shi kudin kai tsaye domin ya kada wa Amurka kuri'a.

An kuma tambaye shi ko kudaden, wanda na aikin kashin-kansa ne, za su yi tasiri kan kuri'ar da zai kada.

Image caption Temarii shi ne shugaban hukumar kwallon kafa ta yankin Oceania

Adamu, wanda shi ne shugaban kungiyar kula da kwallon kafa ta Yammacin Afrika WAFU, sai yace: "Babu shakka, za su yi tasiri sosai.

Temarii, shugaban hukumar kwallon kafa ta yankin Oceania, shi ma an zarge shi da neman a bashi kudi, domin gina wata cibiyar bunkasa wasanni.

Sepp Blatter ya rubuta wasika ga mambobin kwamitin gudanarwa 24, inda yayi alkawarin gudanar da cikakken bincike.

'Ba tare da bata lokaci ba'

Wasikar ta ce: "Ina mai takaicin sanar da ku wani yanayi mai tsauri da muka samu kanmu a ciki sakamakon wani rahoto da jaridar Sunday Times ta wallafa, wanda aka yiwa take da 'kuri'ar sayarwa'.

"Bayanan sun yi mummunan tasiri kan FIFA da kuma yunkurin daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta shekarun 2018 da 2020.

"An ambaci wasu daga cikin mambobin kwamitin na da dana yanzu a zargin."

Ya kara da cewa FIFA... za ta gudanar da cikakken bincike ba tare da bata lokaci ba, karkashin jagorancin kwamitin kula da da'a da kuma Sakatere Janar.

Tuni dai hukumar kwallon kafa ta Oceania tace tana gudanar da bincike kan lamarin.

Temarii, ya bayyana cewa ya yi kuskure wajen tattaunawa da 'yan jaridar da suka yi shigar burtu, game da makomar kuri'arsa.

Ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa ya gana da shugaban FIFA, inda ya nemi ya gudanar da bincike kan zargin da aka yi masa na neman sama da dala miliyan biyu kafin ya kada kuri'a.

Kasashen Ingila da Rasha da kuma hadin guiwar kasashen Netherlands/Belgium da Spain/Portugal ne ke neman damar daukar gasar a shekara ta 2018.

Amurka da Australia wadanda suka fice daga neman daukar nauyin gasar a shekarar 2018, za su maida hankali ne kan gasar shekara ta 2022, tare da Japan da Koriya ta Kudu da kuma Qatar.

Tsohon ministan wasannin Burtaniya Richard Caborn, ya shaida wa BBC cewa ya gamsu da yadda kwamitin da'a na FIFA zai binciki al'amarin cikin gaggawa.