An kashe wasu fursunoni a kasar Haiti

Tambarin Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Tambarin Majalisar Dinkin Duniya a hedkwatarta da ke New York

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun harbe wadansu fursunoni a kasar Haiti, lokacin da fursunonin suka yi garkuwa da wadansu mutane.

Fursunonin dai sun yi yunkurin tserewa ne daga gidan yari mafi girma a kasar, amma yunkurin nasu bai yi nasara ba.

An dai shafe sa'o'i da dama ana musayar wuta a gidan yarin: yayin da hayaki ya turnuke rufin gidan yarin, fursunonin sun kwace makaman da ke hannun masu gadinsu, ciki har da bindiga mai sarrafa kanta, suka kuma fara bude kofofin gidan yarin.

Daga nan ne gungun fursunonin suka yi garkuwa da mutane takwas wadanda suka hada da masu gadi biyar, da ma'aikatan agaji 'yan kasashen waje biyu, da kuma wani akawun gidan yarin.

Daga bisani dai an saki ma'aikatan agajin—dan kasar Sweden daya da ba'Amerike daya.

To amma da hukumomin gidan yarin suka ga alamun gaba daya fursunonin za su tsere sai suka nemi taimako daga Majalisar Dinkin Duniya.

Hakan ne ya sa aka tura motoci masu sulke, da 'yan sandan kwantar da tarzoma, da kuma wata rundunar sojojin Majalisar ta musamman, wadanda cikin 'yan mintuna, tare da taimakon 'yan sandan kasar ta Haiti, suka karbe iko da gidan yarin.

Fursunoni uku ne dai aka kashe wadanda suka yi garkuwa da mutane aka kuma kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su.