Majaisar Dinkin Duniya za ta yi shelar tara kudade ga Nijar

Wasu mata na layi don karbar agajin abinci a Nijar
Image caption Wasu mata na layi don karbar agajin abinci a Nijar

Majalisar dinkin duniya ta ce za ta kaddamar da wani shiri na tara karin kudade ga Jumhuriyar Nijer domin samar da karin abinci ga al'umomin kasar tare da tanadar masu da wani shiri na ayyukan ci gaban kasa mai dorewa.

Sai dai majalisar ta yi gargadin cewar, wajibi ne hukumomin kasar su sa ido sosai a kan karuwar da al'ummar kasar ke yi cikin sauri, wanda ta ce zai iya kasancewa wani tarnaki ga yunkurin da kasar ke yi na yaki da matsalar yunwa.

Wannan sanarwa dai ta biyo bayan ziyarar da mataimakiyar babban sakatare MDD mai kula da harkokin ayyukan jin kai, Mrs Valerie Amos ta kammala jiya a kasar ta Niger.

Akalla mutane miliyan bakwai ne dai suka fuskanci matsalar yunwa a kasar ta Nijer a sakamakon karancin ruwan saman da aka fuskanta a bara.