'Yan Nijar na son karin haske kan kame

A Jamhuriyar Nijar, wasu jam'iyyun siyasa da kungiyoyin farar hula sun yi kira ga hukumomin kasar da su yi wa al'ummar kasa cikakken bayani kan abubuwa da ke faruwa a cikin majalisar mulkin sojin kasar.

A karshen mako ne gwamnati ta cabke, tare kuma da tsare wasu hafsoshin soji hudu da suka hada da tsohon sakataren majalisar mulkin sojan CSRD , Kanar Abdoulaye Bague, da tsohon ministan ayyuka Kanar Amadu Diallo, da Kanar Abubakar Sanda, tsohon shugaban babbar makarantar horas da hafsoshi da kuratan sojoji a Nijar.

Rahotanni sun ce ana zarginsu ne da shirya wata makarkashiyar juyin mulki.