Zanga-zanga ta kara kamari a Faransa

masu zanga zanga a birnin Paris
Image caption Zanga zanga kan karin shekarun ritaya a Faransa

Direbobin manyan motoci a Faransa sun toshe hanyoyi, yayinda zanga-zanga kan sauye sauyen kudaden fansho ta kara kamari a yau, bayan da praministan kasar ya lashi takobin yin duk abinda zai iya ya hana karancin mai.

Masu manyan motocin sun haddasa cunkoson ababen hawa a kan titunan dake kusa da Paris, da kuma birane da dama na lardunan kasar.

Ma'aikatan na nuna takaicinsu ne , na kara yawan shekarun ritaya daga shekaru sittion zuwa shekaru sittin da biyu.

Ma'aikatar zirga zirgar jiragen sama ta bada umurnin soke akalla kashi talatin cikin dari na jiragen da zasu tashi gobe, saboda wannan matsala.