Gangamin adawa da Babangida

Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Image caption Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Yau ne wasu kungiyoyin masu fafutikar kare hakkin bil'adama da kuma tabbatar da dimokuradiyya za su gudanar da wani gangami don nuna adawa da bukatar tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Ibrahim Babangida, ta shiga takarar shugabancin kasar a tutar jam'iyyar PDP.

Kungiyoyin za su gudanar da zanga-zangar ne a karkashin jagorancin fitaccen marubucin nan, Wole Soyinka, da kuma fitaccen lauya Femi Falana.

Kungiyoyin za su fara gangamin ne bayan kaddamar da wata kungiyar gamayya wadda suka sanyawa suna Gamayyar Adawa da Babangida (Anti Babangida Coalition a Turance).

Kungiyar ta ce ta kaddamar da yekuwar yaki da bukatar ta Babangida ne saboda abin da ya aikata na soke zaben 1993, wanda ake zaton marigayi Cif M.K.O. Abiola ne ya lashe shi.

Sai dai wani jigo a kungiyar yakin neman zaben Janar Babangida, Alhaji Danladi Auyo, ya ce tsohon shugaban mulkin sojan ya riga ya yiwa ’yan Najeriya bayanin cewa ba shi kadai ne a bisa radin kansa ya soke wannan zabe ba—Majalisar Koli ta Mulkin Soja ce ta yanke shawarar hakan.

Ya kuma ce Janar Babangida na da ’yancin tsayawa takara.

Wannan dai shi ne gangami na farko da kungiyoyin za su yi, wanda suka kira mafi zafi tun bayan soke zaben na shekarar 1993.