Jam'iyyar CPC ta samu karuwa a jihar kebbi

Jagoran jam'iyyar CPC Janar Buhari
Image caption Jagoran jam'iyyar CPC Janar Muhammadu Buhari

A jahar Kebbi da ke arawa maso yammacin Najeriya, wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP, na bangaren da ke adawa da takarar gwamna Sa'idu Usman Dakin Gari a karo na biyu, sun koma jam'iyyar CPC.

Hakan dai ya biyo bayan kamarin da rikicin da jam'iyyar PDPn ta dade tana fama da shi ne tsakanin magoya bayan gwamna Dakin Gari da kuma masu adawa da shi, wadanda ba sa so gwamnan ya ci gaba da mulkin jihar.

A kwanaki biyun da suka gabata dai, wasu mutane ukku masu neman tsayawa takarar gwamnan jahar ta Kebbi, da kuma shugaban kungiyar yakin neman zaben gwamna Sa'idu Dakin Gari suka koma jam'iyyar ta CPC.

Sai dai a martanin da ta mayar, jam'iyyar PDP ta ce kwadayin mulki ne ya sa suka koma CPCn.

Sauya sheka dai ba bakon abu bane a fagen siyasar Najeriya, musamman ma a lokacin da zaben kasa baki daya ke kara karatowa.