'Yan sandan Faransa sun kwace iko da cibiyoyin adana mai

Zanga-zanga a faransa
Image caption Zanga-zanga a faransa

Gwamnatin Faransa ta yi amfani da jami'an tsaro wajen kawar da toshiyar da masu yajin aiki suka yi wa wasu cibiyoyin adana mai guda uku da ke samarwa da yammacin kasar mai.

Shugaban kasar Nicholas Sarkozy, ya kuma bayar da umarni ga 'yan sandan kasar da su yi amfani da karfi wajen tarwatsa sauran toshiyar da masu zanga-zangar suka yi wa sauran wuraren adana mai a kasar.

Ma'aikatan kasar ta Faransa na yajin aikin ne domin nuna adawar su da shirin yin garanbawul ga tsari fensho na kasar, zanga-zangar da a yanzu ta shiga kwana na bakwai.

Shugabannin kungiyoyin dalibai sun yi kiran da a gudanar da karin zanga-zanga gabanin kuri'ar da 'yan majalisar dattijan kasar za su kada a kan batun nan gaba cikin wannan makon.

Ma'akatan sufuri a kasar sun ce za su ci gaba da bayyana adawarsu da shirin ta hanyar yajin aiki, sai dai babban kamfanin zirga-zirgar jiragen kasan kasar SNCF ya ce, akalla rabin jiragensa za su yi zirga-zirga a ranar Laraba.

Jan daga

Shugaban kasa Sarkozy ya kafe a kan cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da shirin kara yawan shekarun ritayar ma'aikata daga 60 zuwa 62 da kuma daga shekarun samun cikakken fansho na gwamnati daga 65 zuwa 67.

Kusan babu mai a kaso daya bisa uku na gidajen man kasar.

Yajin aikin ya shafi dukkan matatun mai 12 da suke a doron kasar ta Faransa.

Kwanaki biyu kenan a jere ana tuntsurar da motoci a kuma banka musu wuta a birnin Lyon.

An kuma samu tashe-tashen hankula a garuruwan Mulhouse da montbeliard dake gabashin kasar ta Faransa.

Ministan cikin gida na kasar ta Faransa Brice Hortefeux ya ce tashe-tashen hankulan ba abinda za a amince da shi ba ne, domin an raunata akalla 'yan sanda sittin.

Tangarda ga karatu

Yajin aikin gama-garin dai ya shafi sashen ilmi a kasar.

Jami'an sun ce makarantun sakandire 379 ne ko dai aka tshe hanyar isa garesu ko kuma aka samu tangarda a yanayin gudanar da su a ranar Talata.

Wani binciken jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa kimanin kashi 71 cikin dari na 'yan kasar ne suke goyon bayan yajin aikin.

Da alama kuma goyon bayan da shugaba Sarkozy ke da shi a kasar na dada dusashewa.