Mutane biyu sun hallaka a Guinea

Masu zanga-zanga a Guinea
Image caption An rufe kantina da bankuna a birnin Conakry saboda zanga-zangar

Rahotanni sun ce akalla mutane biyu sun rasa rai a Conakry babban birnin kasar Guinea, a tashe-tashen hankulan da suka barke, gabanin zagayen karshe na zaben shugaban kasar da za a yi ranar lahadi mai zuwa.

Rahotanni sun ce an rufe shaguna a wasu unguwannin birnin, sannan babu kowa akan titina.

An dai jiwa mutane da dama rauni, a dauki-ba-dadin da aka yi tsakanin magoya bayan Cellou Dalein Diallo, mutumin da ake ganin zai lashe zaben, da kuma 'yan sanda.

Shugabn 'yan Niger mazauna birnin na Conakry, Alhaji Muhammadu Zako, ya shaidawa BBC ta waya cewa mazauna garin na cikin zaman dar-dar, saboda tashin hankalin da ya faru.

Kasar ta Guinea ta sha fama da rikici a kan wannan zabe, abin da ya janyo a kada dage zaben daga lokacin da aka tsara yinsa tun asali.