An yi gangamin nuna adawa da IBB a Lagos

Daruruwan jama'a sun yi zanga zanga a cibiyar kasuwancin Najeriya, watau Lagos, domin nuna adawa da takarar tsohon shugaban mulkin sojan kasar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, a zaben da za a yi a Najeriyar, a shekara mai zuwa.

Masu zanga-zangar, ta Hadin gwiwar kungiyoyi masu adawa da Babangidan, sun yi kira ga dukkan jam'iyyun siyasar kasar da su guji hada kai da Janar Babangida, saboda a cewarsu, yunkurinsa na sake komawa mulki, cin fuska ne ga martabar Najeriya.

Sai dai magoya bayan Janar Babangida sun ce masu nuna wannan adawa, ba su yi la'akari da tsarin dimokradiyya ba, wanda ya baiwa kowane dan kasa 'yancin tsayawa takarar zabe, da ma kuma yin zaben.