An sallami shugaban hukumar tsaro a Nijar

Janar Salou Djibo
Image caption Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar, Janar Salou Djibo

Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Salou Djibo, ya sallami babban jami'in hukumar tsaro ta farin kaya na kasar.

Ba a dai bayyana dalilan sa suka sa Janar Djibo ya sallami shugaban hukumar tsaron ta farin kaya, Seyni Shekarau, ba.

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan shugaban ya bayar da umarnin tsare mataimakinsa da kuma shugaban rundunar da ke tsaron fadar shugaban kasar bisa zargin kokarin kifar da gwamnati.

Shi dai Janar Djibo ya hau karagar mulkin ne bayan juyin mulkin da sojojin kasar ta Nijar suka yi a watan Fabrariru, ya kuma yi alkawarin mayar da mulki ga farar hula a watan Janairu mai zuwa.