Birtaniya ta zaftare kudaden da take kashewa a kasar

Ofishin neman aiki da tallafi a Birtaniya
Image caption Ofishin neman aiki da tallafi a Birtaniya

Sakataren kula da harkokin kudi na Birtaniya, George Osborne yayi cikakken bayani akan gagarumin shirin gwamnati na zabtare yawan kudaden da gwamnati ke kashewa.

Wannan zaftare kudade ba'a taba ganin irinsa ba a cikin shekaru masu yawa.

Akasarin ma'aikatun gwamnati zasu fuskanci ragin kashi ashirin cikin dari na kudaden da suke samu a cikin shekaru hudu masu zuwa, an kuma yi kiyasin ma'aiaktan gwamnati kamar rabin miliyan ne zasu rasa aikin yi.

Haka nan kuma shekarun yin ritaya daga bakin aiki zasu koma shekaru 66 a madadin 65 a shekara ta 2020.

Gwamnatin hadin gwuiwa ta Birtaniyar ta ce ana bukatar zaftare kudaden ne domin maganin wagegen gibin kasafin kudi na kasar.

To sai dai Jam'iyyar adawa ta Labour da kuma kungiyoyin kwadago sun soki wannan shiri.