An sako dan Burtaniyan da aka sace a Somaliya

Shugaban Somaliya, Sharif Sheikh Ahmad
Image caption Shugaban Somaliya, Sharif Sheikh Ahmad

Kungiyar bayar da agaji ga kananan yara ta Save the Children ta ce an sako wani ma'aikacinta dan kasar Burtaniya wanda aka sace shi a Somaliya.

An saki Frans Barnard ne da asuba bayan wasu manyan gari sun sa baki.

Shi dai Mista Barnard—wanda haifaffen kasar Zimbabwe ne—yana aiki da kungiyar ta Save the Children ne a matsayin mai bayar da shawara ta fuskar tsaro a garin Adado da ke kan iyakar Somaliyan da Habasha.

An kuma yi awon gaba da shi ne daga masaukinsa ranar Alhamis din da ta gabata.

Sai da shugaban hukumar da ke mulkin yankin, Muhammad Aden, da masu gadinsa dauke da makamai suka yi tafiyar awowi a wajen gari kafin su kai wurin 'yan bindigar da ke rike da Mista Barnard.

Mista Aden, wanda ke da karfin fada-a-ji a yankin, shi ne ya sa baki aka saki mutumin.

Sai dai har yanzu babu bayani a kan ko an biya kudin fansa kafin sakin Mista Barnard.

Kungiyar Save the Children ta tabbatar da cewa Mista Barnard na kan hanyarsa ta zuwa wani kebantaccen wuri.