Bukatar karbo bashi ta gamu da cikas a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta yi turjiya ga bukatar Shugaba Goodluck Jonathan ta ciyo wani sabon bashin kusan dala biliyan biyar daga kasashen waje.

A zamanta na jiya ne dai Majalisar Wakilan ta karbi bukatar shugaban kasar ta ciyo wannan sabon bashi wanda ya ce za a yi amfani da shi ne domin gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

Wannan batu dai ya jawo zazzafar mahawara tsakanin 'yan majalisar, kuma hakan ta tilastawa kakakin Majalisar, Dimeji Bankole, ya dage mahawara dangane da batun.

A cewar dan Majalisar Wakilan Dakta Rabe Nasir, akasarin ‘yan majalisar ba su gamsu da dalilan shugaban kasar na karbo rancen ba.

“Aikace-aikacen da aka ce za a yi da su aikace-aikace ne da kasafin kudin da muka yi na wannan shekarar...” zai iya biyan bukata.

Dan majalisar ya kara da cewa “jin wannan bayani ya harzuka ‘yan majalisa, don haka suka yi kukan kura suka nemi su watsar da [batun] kaiwa kwamiti ya duba”.