Mutum guda ya rasu sakamakon rikici a Plateau

Taswirar Nijeriya
Image caption Taswirar Nijeriya

Jami'an 'yan sanda da na gwamnati a Jihar Plateau sun tabbatar da afkuwar wani rikici yau a kauyen Gero, da ke karamar hukumar Jos ta kudu, inda suka ce mutum guda ya rasa ransa, yayin da shanu da dama suka salwanta.

Rikicin ya afku ne a tasakanin makiyaya da kuma Matasa.

Hukumomi a Jihar sun ce suna nan suna gudanar da bincike akan wannan al'amari.

An dai sha fuskantar rikici a karo daban daban a Jihar ta Plateau, wanda kuma ke daukar salo na addini, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.