Birtaniya ta zaftare kudaden da take kashewa a kasar

Ministan kudin Burtaniya, George Osborne
Image caption Ministan kudin Burtaniya, George Osborne

Sakataren Kudin Burtania, George Osborne ya bayyana wani gagarumin shiri na zabtare yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, a wani yunkuri na rage gibin kasafin kudin kasar.

Wannan dai shi ne shirin zabtare kudin da ya fi kowanne girma a Burtaniya tun bayan yakin duniya na biyu.

Mr Osborne ya bayyana cewar gwamnatin gamin gambiza ta Burtaniyar ta kudiri aniyar rage dola miliyan dubu dari da talatin a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Yace: "Yau rana ce da Burtaniya ta dauki gagarumin mataki domin fita daga kangin bashin da ta ke ciki, rana ce ta sake gina kasar ta fuskar tattalin arzuki."

A sakamakon wannan shiri dai, ma'aikatun gwamnati da dama zasu rasa kusan kashi daya bisa hudu na kasafin kudaden da suka saba samu.

Ilimi, harkokin kula da jama'a, sufuri da kuma harkokin 'yan sanda na daga cikin bangarorin da zaftare kudaden za su fi shafa.

Harkokin kasashen waje

Sakataren kudin na Burtaniya ya shaida wa majalisar dokokin kasar cewa za a rage kudaden da ake kashewa a kasafin kudin ma'aikatar kula da harkokin wajen da kashi ashirin da hudu cikin dari.

Yace za'a yi hakan ne ta rage yawan jami'an diplomasiyya dake London, da kuma rage abin da ya kira kanana ayyuka.

Yace za'a maida hankali ga batutuwan kasuwanci, haka nan kuma gwamnati za ta cika alkawarin da ta yi wa Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan agaji.

Mr Osborne yace: "Tallafin da muke bayarwa ga kasashe zai daga zuwa da digo bakwai na kudaden da gwamnati ke samu nan da shekara ta 2013, wanda zai rage yawan mace-macen da ake samu ta cutar zazabin cizon sauro da rabi a kasashe masu tasowa."

Suka da adawa

Babbar jam'iyyar adawa ta labour ta bayyana shirin gwamnati gamin gambizar da cewa mummunar caca ce.

Mai magana da yawun jam'iyyar Alan Johnson ya shaida wa zaman majalisar dokokin burtaniyan cewa, zaftare kudaden gwamnatin su ne mafi girma a tarihin kasar, kuma an yi su ne saboda akida ba don dalilai na tattalin arziki ba.

Mr. Johnson ya kuma musanta ra'ayin da gwamnatin gamin gambizar ta bayyana na cewa, burtaniya na dab da talaucewa karkashin gwamnatin Labour da ta gabata, wadda ta fadi zabe a watan Mayun da ya gabata.

Sakataren kudin na Burtaniya, ya bayyana cewa gwamnatinsu za ta zaftare pam biliyan bakwai daga kudaden tallafin da ake baiwa al'ummar kasar.

Za kuma a kara yawan shekarun ritayr ma'aikata.

BBC

Ita ma tashar BBC an shaida mata cewa za a dakatar da kudaden da ake karba daga masu akwatin talabijin a Burtaniya da ake kira license fee har na tsawon shekaru shida.

Kuma nan gaba tashar BBC mai watsa shirye-shiryenta ga kasashen duniya wato World Service za ta koma samun kudaden shigarta ne daga kudaden licence fee, maimakon daga ma'akatarharkokin wajen Burtaniya kamar yadda lamarin yake a yanzu.

Hakan dai na nuna raguwar kusan kashi goma sha shida cikin dari na kudaden shigar da BBC ke samu.

Sai dai gwamnatin gamin gambizar ba za ta zaftare kudaden fannin lafiya, da taimakon da take baiwa kasashen duniya ba.

Gwamnatin ta gamin gambizar ta ce, matakin na zabtare kudaden shigar ba lallai ne ya cike gibin kasafin kudin gwamnatin a tsawon wannan lokaci ba, to amma zai rage gibin matuka.

Sai dai kungiyoyin kwadago da jam'iyyar adawa ta Labour da ma wadansu masana tattalin arziki sun zargi gwamnatin da yin ganganci.

A cewarsu, wannan mataki ba abin da zai haifar sai sake jawowa kasar koma-bayan tattalin arziki.

Rahotanni sun ce gwamnatin ta yi hasashen mutanen da za su rasa ayyukan yi sakamakon wannan mataki sun kai dubu dari biyar.

Karin bayani