Birtaniya ta sakawa bankuna sabon haraji

Kwana guda bayan sanarda wani gagarumin zaftare kudaden da take kashewa da ba'a taba yi ba a shekarun baya, gwamnatin Birtaniya ta wallafa cikakkun tsare tsarenta na sanya sabon haraji ga bankunan 'kasar da ake saran zai samarda kimanin dala biliyan hudu a kowacce shekara.

Ministan harkokin kudi ya ce an dauki matakin ne da nufin karfafa gwuiwar bankuna akan su rage fadawa cikin hadari.

Kawo yanzu dai ba'a kayyade adadin yawan kudaden da za'a rika karba a matsayin harajin ba.

Wakilin BBC ya ce wata sanarwa data fito daga ma'aikatar baitul malin kasar ta ce yana da muhimmanci bankunan su samar da wani kaso saboda irin hadurran da suke janyowa tattalin arzikin kasar.