An gurfanar da Charles Okah a Kotu

Hukumar leken asiri ta Nigeria, watau SSS, ta gurfanar da wasu mutane hudu a gaban wata kotun Magistrate yau a Abuja, inda ta ke zarginsu da laifin da na bomb din da aka yi a Abuja, babban birnin kasar, ranar da kasar ke bukin cika shekaru hamsin da samun 'yan cin kanta.

Mutanen da aka gurfanar sun hada da Charles Okah, dan uwa ga Mr Henry Okah, wanda shi ma aka gurfanar a gaban wata kotu a Africa ta Kudu, inda ake zarginsa da samun hannun wajen dana bomb din.

Bomb din dai yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla goma, yayin da wasu suka samu raunuka.

An dai gurfanar da mutanen ne cikin tsauraran matakan tsaro.