Yan kwadagon Faransa sun ce ba-gudu-ba-jada-baya

Zanga-zanga a Faransa
Image caption Kusan mako guda kenan ana yajin aikin

Ma'aikatan kwadago a Faransa sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga a wani bangare na nuna adawa da sabon tsarin fansho da gwamnati ta bullo da shi.

Bernard Thibault, shugaban kugiyar kwadago ta CGT, shi ya bayyana hakan a daidai lokacin da 'yan kwadagon ke tattauna yadda za a ci gaba da zanga-zanga a rana ta bakwai.

A yanzu haka kuma ana ci gaba da yajin aikin nuna adawa da shirin gwamnati na kara shekarun ajiye aiki daga 60 zuwa 62.

Toshe matatan mai da cibiyoyin adana shi ya haifar da karancin mai a kasar.

Shugaba Sarkozy ya yi kira da akawo karshen matsalar. "Wannan doka wacce ke da nufin durkusar da kasar mu, za ta iya haifar da rashin ayyukanyi da koma bayan tattalin arziki."

Mr Thibault ya gayawa gidan rediyon RMC: " Gwamnati ba ta da niyyar saukaka al'amura. Muna bukatar ci gaba da zanga-zanga a mako mai zuwa ba tare da bata lokaci ba.... Za mu nemi ma'aikata da su ci gaba da yajin aiki tare da fitowa kan tituna."

A garin Marseille mai tashoshin ruwa da ke kudancin kasar, babu hanyoyin sadarwa na gwamnati da kuma jiragen kasa.

Wakilin BBC Matthew Price ya ce, halin da ake ciki a birnin Marseille ka iya jefa kasar cikin rudani.