An samu yunkurin juyin mulki a Nijar

Shugaba Saliou Djibo
Image caption YUnkurin juyi ya ci tura

Kaka gwamnatin mulkin soji ta Nijar, Kanar Abdulkarim Goukoye, ya ce gwamnatin kasarn ta bankaro wani yunkuri na hambarar da gwamnati.

A ta bakin kakakin, wadanda suka yi shirin juyin mulkin sun yi aniyar hallaka har shi kansa shugaban kasar na yanzu.

Ya ce idan da wadanda suka shirya makarkashiyar sun yi nasara, da sun sauya akalar shirin gwamnatin mulkin soji ta yanzu game da maida mulki hannun farar hula.

Da ma dai cikin 'yan kwanakin da suka wuce, gwamnati tana ta kame-kamen wasu tsaffin kusoshin gwamnatin kasar.