EFCC ta ce ana barazanar kai mata hari

Image caption Taswirar Najeriya

Hukumar da ke yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati wato EFCC, ta yi zargin cewa wadansu na barazanar hallaka jami'anta, da kuma shugabar hukumar, Madam Farida Waziri ta hanyar tada bama bamai a harabar hukumar dake Abuja.

Kakakin hukumar, Mista Femi Baba Femi ya bayyana haka a wata takarda da ya aikewa kafofin yada labarai.

Sanarwar ta Mista Femi dai na yin Allah Wadai ne da abinda hukumar ta kira jerin barazanar hallaka shugabar hukumar da kuma wadansu kusoshin hukumar ta EFCC.

Hukumar ta bayyana cewa a ranar ashirin ga watan da muke ciki ta samu sakonni ta wayar hannu wato text har ashirin da ke cewa za'a kai jerin hare- haren a ofishin hukumar dake Abuja.

Hukumar ta ce wadansu daga cikin sakonnin na kira ne ga jama'a da su kauracewa ofishin EFCC din a ranar shida ga watan Nuwamba mai kamawa, domin a ranar ne sakon ke bayyana cewa za'a kai wa ginin hukumar harin.

Kawo yanzu dai ba'a san ko su waye suka aiko da sakonnin ba, sai dai kuma hukumar ta bayyana cewa ba ta dauki wannan barazanar da wasa ba, tuni ta baza jami'anta domin yin bincike akai.

Hukumar dai ta sha alwashin cewa lallai nan ba da jimawa ba za ta zakulo ko su waye ke da hannu a wannan al'amari.

Wannan dai na zuwa ne dai dai lokacinda ake cigaba da nuna damuwa akan yanayin tsaro a Najeriyar.