Takaddama kan rijiyoyin mai tara a Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A Najeriya, wata takaddama ta kunno kai a kan wadansu rijoyoyin mai guda tara da shugaban kasar ya amince a baiwa jihar sa ta haihuwa, wato Bayelsa.

Rohotanni sun ce shugaban ya amince a baiwa jihar rijiyoyin ne da ke kusa da gabar teku bayan da gwamnatin jihar ta rubuto masa bukatar mallakar rijiyoyin.

Hakan kuma na nufin jihar za ta fi kowacce jiha samun kudaden shiga a kasar.

Masu lura da al'amura da ma masana kundin tsarin mulki dai na ganin hakan ya sabawa dokar rabon arzikin kasa ta shekarar 2004—wadda ta tanadi baiwa jihohin da ake samun mai daga gare su kaso goma sha uku cikin dari na kudaden man—suna masu cewa majalisar kasa ce kadai ke da ikon yin kari ko ragi a kan abin da wata jiha ke samu.

A ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata ne dai shugaban ya amince a baiwa jihar ta Bayelsa kashi shida cikin dari na kudin da ake samu daga danyen man fetur din da aka hako daga wadannan rijiyoyi, sakamakon bukatar da jihar ta gabatar masa a ranar 16 ga watan Fabrairu, lokacin yana mukaddashin shugaban kasa.