An zargi China da shigar da makamai Darfur

Dakarun kiyaye zaman lafiya a Darfur
Image caption Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Darfur

Jami'an diflomasiyya a Majalisar Dinkin Duniya sun ce China na kokarin hana wallafa wani rahoto wanda ya yi zargin cewa an yi amfani da albarusan kasar ta China a kan dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar a yankin Darfur da ke kasar Sudan.

Majiyoyi da dama sun ambato rahoton yana cewa an samu kwanson albarusan da suka fito daga China masu yawa a wuraren da aka kai hari kan dakarun kiyaye zaman zaman lafiya na Majalisar.

Sai dai ga alamu babu wata kwakkwarar hujjar da ke tabbatar da cewa China ta sayar da wadannan albarusai kai tsaye ga gwamnatin Sudan ko kuma cewa kasar ta China tana da masaniya a kan cewa za a yi amfani da su a Darfur ne.

Kasar ta China ta yi watsi da wannan zargi.

Wani jami'in diflomasiyyar China, Zhao Baogang, ya ce rahoton cike ya ke da kusakurai.

Jami'an diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya dai sun zargi China ne da kokarin hana wallafa rahoton, wanda wani kwamitin kwararru ya rubuta, kuma a bisa al'ada za a wallafa a yanar gizo bayan gabatar da shi ga Kwamitin Sulhu na Majalisar.

Kwamitin ne dai ke sa ido a kan jerin takunkumin da Majalisar ta kakabawa Sudan a shekarun 2004 da kuma 2005, ciki har da wanda ya haramta sayarwa Sudan din makaman da za ta yi amfani da su a yankin Darfur.

Sayarwa Sudan makamai dai ba laifi ba ne amma in gwamnatin kasar ta bayar da tabbacin cewa ba za ta yi amfani da su a yankin na Darfur ba.

Rahoton ya kuma bayyana cewa an gano wasu nau'uka biyu na kwanson albarusai wadanda aka kera a Isra'ila.