Ambaliyar ruwa ta shafi dubban jama'a a jamhuriyar Benin

Jamhuriyar Benin a taswirar Afirka
Image caption Jamhuriyar Benin a taswirar Afirka

Ambaliyar ruwan da aka yi a jamhuriyar Benin ta shafi kimanin mutane dubu 700, in ji Majalisar Dinkin Duniya. Dubban mutane sun rasa matsugunnan su, yayin da ake fargabar barkewar cututukan da ake samu ta ruwan sha. Tuni aka samu mutane 800 da suka kamu da cutar kwalara.

Dr. Suleiman Diallo, wakilin asusun kula da kananan yara na UNICEF a birnin Cotonou na Benin din, ya ce akwai matukar fargabar barkewar annoba. Akwai kuma matsalar cututukan da suka shafi rashin abinci mai gina jiki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kawo yanzu mutane 60 ne suka mutu a ambaliyar ruwan.