Majalisar dattijan Faransa ta amince da dokar Fansho

Majalisar dokokin Faransa ta kada kuri'ar amince da sabuwar dokar Fanshon da ke jawo zanga-zanga da tashin hankali a kasar.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da kungioyin kwadago ke yajin aiki a duk fadin kasar, domin nuna adawa da dokar, wacce ke son a kara shekarun ajiye aiki daga 60 zuwa 62.

Sanatoci 177 ne suka amince da dokar yayinda 153 suka kada kuri'ar rashin amincewa da ita. Hakan dai ya faru ne bayan da gwamnati ta bullo da wata dabara ta musamman domin hanzarta kuri'ar.

A yanzu dokar na bukatar amincewar majalisun kasar biyu da kuma babbar majalisar tsarin mulki ta kasa, kafin ta zamo doka.