Mutane 155 sun rasu sakamakon annobar Kwalara a Haiti

Jami'an kiwon lafiya a Haiti sun ce akalla mutane 155 sun rasa rayukansu, sakamakon abun da yanzu shugaban kasar Rene Preval ya tabbatar cewa Kwalara ce.

Mutane fiye da dubu daya da dari biyar ne suka kamu da cutar ta Cholera a wani yanki dake Arewacin Port au Prince, babban birnin kasar, kuma wannan shi ne bala'i mafi girma da kasar ta fuskanta tun bayan mummnar girgizar kasar da aka yi a cikin watan Janairun da ya gabata.

Asibitocin yankin sun cika makil da marasa lafiya, wadanda ke fama da mai da gudawa.