Wikileaks ya wallafa bayanai game da Iraqi

Wikileaks
Image caption Wikileaks

Dubban bayanan sirri na Amurka da shafin yanar gizo na Wikileaks ya wallafa na nuna cewa manyan kwamandojin sojin Amurka na sane da cewa dakarun Iraqi na muzgunawa fursunoni amma ba su dauki wani mataki a kai ba.

Bayanan sun bayyana irin azabtarwa da kuma cin zarafi da ma kisan gillar da dakarun Iraqin ke yiwa wadanda suka tsare din.

Bayanan sun nuna cewa dakarun sojin Amurka kan rubuta rahotanni ga manyansu amma su kan umarcesu da kar su yi bincike akai.

A wani wuri bayanan sun nuna yadda aka baiwa wani jirgin helikopta izinin bude wuta kan wasu mayakan Iraqi da ke yunkurin mika wuya ga Amurka.

Akwai kuma wasu da ke nuna irin rawar da Iran ta taka wurin baiwa masu fafutukar makaman dakarunta na juyin juya hali.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton dai ta fito ta yi Allah Wadai da wannan sirri da shafin Wikileaks din ya tona.

Misis Clinton dai ta bayyana cewa wannan ka iya jefa rayuwar 'yan Amurka da sauran kawayensu a cikin kasada.

Gwamnatin Amurka musamman ma'aikatar tsaron kasar, ta yi ta kokarin ganin cewa wannan kundin bayanan wanda ke dauke da kimanin shafuka dubu dari hudu, wanda ke da nasaba da yakin Iraqi bai bayyana ba.

Wannan dai yanzu haka ya dankwafe nauyin wasu bayanai makamantan wannan da shafin na Wikileaks ya wallafa a baya game da rikicin dake faruwa a Afghanistan.