Zazzabin cizon sabro na cigaba da kisan jama'a

Sabro
Image caption Sabro

Zazzabin cizon sabro ko malaria, cuta ce da ke hallaka mutane miliyan 1 zuwa 3 a kowace shekara, kamar yadda kiyasi ya nuna.

Galibinsu kuma kananan yara ne a kasashen Africa da ke yankin kudu da hamadar Sahara.

An kuma yi kiyasin cewa, zazzabin yana haddasa asara wadda ta kai kimanin dala miliyan dubu 12 a kasashen Africa a kowace shekara.

Rashin tsabtar muhalli na daga cikin abubuwan da ke janyo zazzabin cizon sabron.

Rage yaduwar cutar nan da shekaru 5 masu zuwa, na daga cikin muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya.

Baya ga masu sauraro, daga cikin bakin da mu ka gayyato a shirin na Ra'ayi Riga har da Dokta Muhammad Sadiq, babban jami'in hukumar Lafiya ta duniya, WHO, wanda ke kula da yaki da cutar zazzabin cizon sabron a sashen arewa maso yammacin Najeriya.

Akwai kuma Dokta Mansur Kabir, babban jami'i a ma'aikatar kula da lafiya ta tarayya a Najeriya.