Dubban dalibai ne suka kasa shiga jami'a a Burtaniya

Ilimi
Image caption Wasu dalibai da suka gama karatun jami'a

Wani rahoto da hukumar tallafawa daliban da ke son shiga jami'a a Burtaniya, ya ce a bana kusan dalibai dubu 190 ne suka rasa damar shiga jami'a a kasar.

Shugaban hukumar Mary Curnock ta yi gargadin cewa, tururuwar da dalibai za su yi domin kaucewa karin kudin makarantar da ake hasashen yi badi, zai kara matsin lamba kan jami'o'i a shekara mai zuwa.

Kudaden makarantar wadanda aka takaita kan fan 3, 290 a Ingila da Wales da Ireland ta Arewa, ana sa ran za su karu idan gwamnati ta amince da rahoton Lord Browne wanda yayi nazari kan makarantun gaba da Sakandare.

Ya bada shawarar a kawar da takunkumi kan kudaden makaranta, da tallafin da ke sanyawa a takaita kudaden makaranta su zamo kasa da fan 7000.

Kungiyar dalibai ta kasa ta zargi rahoton na Lord Browne da karawa dalibai adadin kudin da suke biya, domin cike gurbin da tsuke bakin aljihun da gwamnati ta kirkiro zai haifar.

A ranar Laraba ne gwamnati ta sanar da rage kashi 40 cikin dari na tallafin da take baiwa manyan makarantu, a wani bangare na rage kudaden da take kashewa, tana mai saran kudaden da ake samu daga dalibai su maye gibin da za a samu.