Tsuke bakin aljihun Birtaniya zai shafi Afirka

Wasu masana harkar da ta shafi tattalin arziki a Najeriya, na ganin cewa tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka zai iya fuskantar matsaloli a sanadiyyar matakin tsuke bakin aljihun da gwamnatin Birtaniya ta dauka.

Matakin da gwamnatin Birtaniyan ta dauka dai ya kunshi rage kashe kudade.

Wannan kuma wani yunkuri ne na rage gibin da Birtaniyan ta samu a kasafin kudinta da kuma rage basussuka da gwamnati ta ciyo.

Sai dai kuma wannan matakin kamar yanda masana suka bayyana shi, wanda ake gani zai iya janyowa kimanin mutane miliyan daya rasa ayyukansu, zai shafi 'yan asalin nahiyar Afirka da dama wadanda ke zaune a can.

Kuma wannan kamar yanda masanan suka bayyana na nufin samun koma baya a kudaden da su kan aiko gida.

Masanan dai sun bayyana cewa wannan zai sanya ala tilas gwamnatocin nahiyar Afirka su fuskanci babban kalubale na inganta yanayin zama, domin a amfana da iliminin da kwararrun nahiyar ke dashi, wadanda ke barin kasashen su domin neman aiki a kasashen da suka ci gaba kamar irinsu Birtaniyan