An sami barkewar tashin hankali a Guinea

Rikicin siyasa a Kasar Guinea
Image caption An samu barkewar tashin hankali a kasar Guinea bayan da aka dage zaben shugabankasar zagaye na biyu

An samu barkewar tashe tashen hankula a kasar Guinea bayan da aka dage zaben shugaban kasar zagaye na biyu da aka shirya gudanarwa ranar lahadi.

Rahotanni sunce magoya bayan 'yan takarar shugaban kasar biyu, Cellou Dalein Diallo da Alpha Conde sun yi arangama a wasu tituna a Conakry, babban birnin kasar.

Zaben da aka dage dai shine ake saran zai kasance zabe na farko da zai mayar da kasar kan turbar dumukradiyya.

Sai dai shugaban hukumar zaben ya ce ba zai yiwu a iya gudanar da zaben ba kamar yadda aka tsara, sai anan gaba za'a sanarda da sabuwar ranar da za'a yi zaben.

An dai yi ta gargadin cewa jinkirta zaben shugaban kasar zagaye na biyu ka iya haifar da rashin zaman lafiya a kasar ta Guinea.