Mutane 7 sun mutu a wajen kallon kwallo a Kenya

Wasan kwallon kafar Kenya
Image caption Mutane sun mutu yayin wani turmutsitsin shiga filin wasan kwallon kafa a Kenya

A kalla mutane bakwai ne suka mutu a wani turmutsitsi a filin wasan kwallo kafa a kasar Kenya.

Lamarin dai ya auku ne a dai dai lokacin da magoya bayan wasu kungiyoyi biyu ke kokarin shiga filin wasa don kallon fafatwar da aka yi tsakanin wasu kungiyoyin wasa biyu da suka yi fice a kasar.

Wani jami'in kungiyar Red Cross ya ce an kashe shida daga cikin mutanen ne a babban filin wasa na Nyayo dake Nairobi, ya yinda cikon na bakwansu ya mutu a asibiti.

Lamarin dai yasa sai da aka dakatar da wasan da aka fafata tsakanin Gor Mahia da kuma AFC Leopards na wani dan lokaci, inda masu ayyukan bada agaji suka taimaka wajen kwashe wadanda suka samu raunuka.