A Najeriya, ANPP ta ce za ta fita daga gwamnati

ANPP
Image caption ANPP

A Najeriya, babbar jam'iyar adawa ta ANPP, ta yi karin haske akan dalilanta na son ficewa daga gwamnatin hadin kan kasa, karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan.

Jam'iyar ANPP din dai ta ce gwamnati ta ki ci gaba da mutunta yarjejeniyar da suka kulla da jam'iyar PDP, a lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar adua ke shugabanci, inda a ka baiwa jam'iyyar ta ANPP mukaman ministoci da dama a kasar.

Jam'iyyar ANPP ta ce shugaba Jonathan ya yi watsi da yarjejeniyar, inda ya bar ta da ministoci biyu kadai.

ANPP din dai ta bayyana cewa ficewa daga cikin gwamnatin hadin kan kasa zai bata damar yin adawa sosai da jam'iyyar PDP da ke mulkin kasar, domin kawo sauye sauye masu amfani.

Sai dai a wani martanin da jam'iyar PDP ta mayar, ta ce ficewar jam'iyar ANPP ba zai yi wani tasiri a tsarin mulkin Najeriya ba.