Majalisar Dinkin Duniya zata kai agaji Benin kan ambaliyar ruwa

Hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da 'yan gudun hijira ta ce, a wannan satin zata soma kai tantuna ta jiragen sama a jamhuriyar Benin, inda aka yi ambaliyar ruwan da ba a taba gani ba a tarihin kasar.

Ambaliyar ta shafi kashi biyu cikin ukku na kasar ta Benin. Kimanin mutane dubu dari bakwai ne suka rasa gidajensu:

A cewar jami'ar kungiyar agajin CARE, mutane na zaune a kan dakunansu, ko kuma a cikin kwale-kwale, kusa da gidajensu.

Hukumar kula da 'yan gudun hijirar za ta kai tantuna dubu ukku a birnin Cotonou.

Wata mai magana da yawun majalisar dinkin duniya a Cotonoun ta shaidawa BBC cewa, mai yiwuwa har yanzu ba a rabu da Bukar ba, ganin cewa a watan Nuwamba ne ake sa ran cewa, ruwan saman zai kai yankin arewacin Benin din.

Kawo yanzu mutane dari takwas sun kamu da cutar kwalara, kuma yawansu na karuwa a kowace rana.