An kara samun tashin hankali a kasar Guinea-Conakry

An kara samun tashin hankali a kasar Guinea-Conakry, inda aka dage gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasar har sai abinda hali yayi, saboda taho-mu-gamar da aka rika yi tsakanin magoya bayan 'yan takarar biyu, Cellou Dalein Diallo da Alpha Conde.

An ce mutane dayawa sun jikkata, kuma an wawashe kantuna a birnin Kissidougou.

Sai dai tun daga jiya Asabar, tashin hankalin ya lafa a galibin yankunan kasar ta Guinea, ciki har da Conakry, babban birnin kasar, bayan da 'yan takarar biyu suka yi kiran a kwantar da hankula.

Shugaban mulkin sojan Guinean, Janar Sekouba Konate yayi gargadin cewa, ba za a kyale mutanen da ke aikatar miyagun laifufuka ba.